Breaking

Wednesday, September 18, 2019

Yadda Zaka Duba Number Wayarka Alayin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile


Darasinmu nayau shine yadda zaka gano kokuma kaduba lambar layinka, Wani lokaci zakaga mutum yasayi layin waya amma baisan lambar layinba. Insha Allah yau zamu kawo yadda zaka duba lambar layinka.


Dayawa yana faruwa kana da layi bakasan lambar layin ba, Bugu da kari a wannan lokaci layuka dayawa basa zuwa da lambar waya a rubuce. Saboda da kaha muka rubuta wannan post muna fatan zai amfaneku.


Idan kana amfani da layin MTN kana so kasan lambar layin,  Sai kadanna *663# akan wayarka MTN zasu tura maka sako mai dauke da lambar wannan layi.


Idan kana amfani da layin Airtel kuma ga yadda zaka duba lambar layinka, Kawai kadanna *746# akan wayarka nantake zakaga lambar wannan layi.


Masu amfani da layin Glo zasu iya duba lambar layinsau idan suka danna *135*8# akan wayarsu zasu ga lambar wannan layin insha Allah.Idan kana da layin Etisalat kokuma 9Mobile a yanzu kuma kana so kaduba lambar layin ga yadda zakayi, Sai kadanna *248# akan wayarka zakaga lambar layinka.Wannan sune lambobin da ake duba Number akan layin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile Muna fatan wannan post zai Yi muku amfani. Sai kukasance da wannan website akoda yaushe domin abubuwa masu amfani, Mungode.


No comments:

Post a Comment