Breaking

Wednesday, September 18, 2019

Yadda Zaka Duba Data Balance Alayin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile


Idan kana bukatar sanin yadda ake duba data balance wato adadin data ko mb dake cikin layinka yau zaka sani insha Allah, 


Dayawa suna sayen data ko mb da layinsu amma basu san yadda ake dubawa ba, Kuma sanin hakan yana da muhimmanci domin zaka san adadin data dake cikin layinka da kuma yawan wanda kayi amfani dasu.Yau zamu kawo muku hanyoyin daza kuduba data balance alayiku na MTN Airtel Glo 9Mobile dake Nigeria sai kubiyo mu.Zamu fara da masu amfani da layin MTN, Idan kana so kasan adadin data dake Cikin MTN sai kadanna *131*4# akan wayarka nan da nan zaka gani.


Sai kuma masu Airtel idan suna so su duba data balance sai su danna *140# akan wannan layi zasuga adadin data dake kan layin.


Munzo gun masu layin Glo idan kanada data akan layinka na glo kuma kana so kasan adadinta sai kadanna *127*0# shikenan zakaga yawan data balance dinka.


Zamu kare wannan bayani da masu amfani da layin Etisalat ko 9Mobile, Domin duba data balance akan 9Mobile kawai sai kudanna *228# akan wayarku zaku gani insha Allah.


Wannan shine karshen wannan post muna fatan wannan rubutu zai amfaneku domin duba data balance alayunka,  Mungode.

No comments:

Post a Comment