Breaking

Wednesday, September 11, 2019

Manyan Websites 2 Dazaka Iya Bude Blog Ko Website Kyauta

Wadannan website 2 suna bada dama ga wanda yake son bude website kyauta kokuma yabiya wasu kudi domin bude mai kyau

Kamar yadda yazama ruwan dare kirkirar website ko blog a wannan zamani saboda neman kudi a internet, kusan a kullum sai an kirkiri website masu yawa wanda idan aka gaya maka adadin sai kace qaryane wanda kuma zaka iya bude naka kyauta.


Mutane dadama suna bude website ko blog domin neman kudi a internet kokuma wata manufa mai kama da haka, Idan kana bukatar bude website ko blog kyauta wannan rubutu zai maka amfani.


Akwai gurare guda 2 wanda suka shahara domin bude website wanda kusan kaso 80 cikin 100 anan suke kirkirar website dinsu domin fara kasuwancin a internet. 


Wadannan website 2 suna bada dama ga wanda yake son bude website kyauta kokuma yabiya wasu kudi domin bude mai kyau kamar wordpress.  Blogger kuma baka bukatar kashe ko Naira domin bude blog akanta.Websites Guda 2 Dazaka Iya Bude Website Ko Blog Kyauta

(1) Blogger
Kamar yadda nafada abaya cewa blogger kyauta ce baka bukatar kashe kudi,  Haka abin yake idan kana bukatar bude blog a blogger kawai kaje kayi register da Gmail Account dinka nan take zaka bude free website a blogger. 


Sai dai idan kana son blog dinka yakayatu sosai zaka iya sayen Template wato Designed na website sannan kasayi custom domain kamar  .Com ko .Com.NG domin karawa blog dinka nagarta dakuma inganci.


(2) Wordpress
Wannan ita kuma tana da hanyoyi 2 na bude website wato akwai na kudi akwai kuma na kyauta,  Idan kana so kabude na kyauta to zasu dora maka talla akan website dinka wanda kabude daga gurinsu. 


Idan kuma kana son bude na kudi to ana sayen Hosting da kuma custom domain domin dorawa akan wordpress saboda website dinka yazama naka nakanka sannan kuma baka da wata matsala. 


Da wadannan website zaka iya bude website ko blog sannan kafara neman kudi a internet na kyauta ko na kudi. Sannan akwai abin daya kamata kasani shine idan kasayi Hosting ko custom domain to duk shekara zaka sabunta wannan kudi kokuma website dinka yadaina aiki.


Wannan shine karshen wannan post muna fatan wannan rubutu zaiyi muka amfani wajen bude website ko blog a blogger ko wordpress domin fara neman kudi a internet.  Mungode.
No comments:

Post a Comment