Breaking

Saturday, September 14, 2019

MTN Extra Time: Yadda Zaka Aro Airtime Alayin MTN


Wasu lokata Airtime yana karewa mutum kuma babu inda ake sayarwa a wajen dayake, saboda haka kamfanin MTN yakawo wani tsari wanda zaka iya aran kudi idan kana bukata daga baya sai kabiya.


Wannan tsari yazo da sauki a wajen wasu yayin da wasu kuma suke ganin ba daidai baneba. Domin tsarin zai baka damar aro airtime lakacin daba dashi sai akwai wani kaso da MTN yake cirewa a duk lokacin daka ari kudi.


Kamar yadda suka MTN suka tsara lamarin shine idan karanci N100 to akwai service fee N15 wato zaka samu N85 kenan sannan kuma idan kazo biya N100 zaka biya.


Haka abin yake idan karanci N50 zaka samu N42.5 wato service fee N7.5 duk lokacin daka saka airtime MTN zasu janye kudin daka aro batare da bata lokaci ba.


Yadda Zaka Aro Airtime Alayin MTN

Idan kana son shiga wannan tsari zaka danna *606# zakaga shafin daza aro airtime da layinka na MTN.Amma bakowane layi MTN suke bawa aro ba, Sannan akwai adadin jimawa da layin zaiyi kafin yafara samun aron airtime.Idan kadanna *606# akan wayarka zakaga duk wani bayani daga MTN, Idan layinka yana cikin wanda zasu samu aron airtime zaka gane.Idan kuma baya ciki sai kajira sannan kacigaba da saka Recharge Card har kakai matakin daza kasamu aron airtime da layinka.


Wannan shine bayani akan yadda ake aro airtime daga layin MTN, Muna fatan wannan bayani zaiyi muku amfani, Mungode.No comments:

Post a Comment