Breaking

Tuesday, September 10, 2019

Hanyoyi 5 Da Ake Samun Kudi A Internet Online | Insurance Press

Hanyoyi 5 Da Ake Samun Kudi A Internet Online

Yanzu neman kudi yazama mai sauki sosai yadda zaka iya samun da wayar dake hannuka Android kokuma Laptop.  Ana samun kudi Cikin sauki ta internet wanda idan ana baka labari sai kace qaryane. 


Maganar gaskiya shine ana samun kudi a internet sosai da sosai,  Amma abu mafi wahala shine ba kowa yasan yadda ake samun kudi a internet ba, Yau zan nuna wasu hanyoyi wanda idan kabisu zaka samu kudi a internet. 


Kafin na nuna maka wadannan hanyoyi yakamata kasan wani abu shine duk hanyar dakasan ana samun kudi da ita a internet to tana bukatar kayi aiki sosai kafin kayi nasara, Wato idan kana bukatar samun kudi lallai sai ka maida abin kamar kasuwanci na zahiri. Hanyoyi 5 Da Ake Samun Kudi Dasu A Internet


(1) Blogging
Abin dayasa nafara kawo wannan hanya saboda tayi kaurin suna sosai wajen neman kudi a internet, ma'anar Blogging shine bude website domin samun kudi akwai gurare dayawa a internet da ake bude website wasu Kyauta wasu kuma sai kabiya kudi.


Idan kana bukatar bude website zaka iya zabar wajen kamar Blogger (Kyauta Ce) ko Wordpress (Sai Da Kudi) domin kirkirar website dinka sannan kafara samun kudi a internet.


(2) YouTube
Hanya ta biya itace YouTube wajen kallon videos, Ana samun kudi a YouTube idan kabude channel sannan kana dora video idan channel dinka yakai wani mataki zaka fara samun kudi.


Babu shakka wajen samun kudi a YouTube abin kawai dakake bukata shine bude channel wanda kyauta ne sannan idan channel dinka yasamu Subscribers 1000 da watch hours 4000 YouTube zata duba wannan channel idan bashi da wata matsala natake zaka fara samun kudi.


(3) Social Media Marketing
Wannan hanya tana nufin kasuwanci a kafafen sadarawa na internet, Wannan hanya ana samun kudi da ita sosai idan kana da mutane a profile dinka na social media.  Social Media shine kamar Facebook,  Twitter, Instagram, Watsapp da sauransu.


Ana samun kudi da social media marketing ta hanyar daukar talla daga wani kamafani idan aka sayi kayansu kaikuma zaka samu wani kaso daga ciki. Sannan idan kana da wani abu dakasan mutane zasu iya saya zaka iya talla tashi ta social media domin samun kudi.


(4) Freelancing
Wannan shi ake kira kodago wato kayiwa wani aiki yabiyaka kudi,  Masu samun kudi da wannan hanyar suna shiga internet domin nemo wani dasuka iya idan sukayi sai a biyasu.


Zaka iya samun kodago a internet a gurare da dama kamar facebook ko watsapp,  Sannan akwai websites da aka bude musamman domin masu yin freelancing sune kamar: fiverr, upwork, shareskill.  da sauransu.


(5) Affiliate Program
Wannan hanya tana da saukin samun kudi a internet,  Ma'anar wannan hanya shine wani mutum ya yadda zaiyi talla a wani kamfani idan aka sayi kayan wannan kamfani sai abiyashi wani abu daga ciki.


Akwai kamfani dayawa wanda suke da tsarin Affiliate Program wanda zaka iya Register dasu domin samun kudi a internet,  Sannan wannan kasuwanci yana da sauki abin kawai daza kayi shine kayi join da wadannan website masu tsarin affiliate program sukuma zasu baka link duk sanda wani yabi ta wannan link yasayi wani abu to kaikuma zaka samu wani abu daga ciki.


Wannan sune hanyoyi guda 5 wanda muka yi alkawarin kawo muku muna fatan zakuyi amfani da wadannan hanyoyi domin neman kudi a internet. Mungode.


No comments:

Post a Comment