Breaking

Sunday, September 15, 2019

Airtel Night Plan: Yadda Ake Night Browsing Da Layin Airtel 1GB @N100 500MB @N50


Yau zamuyi bayani akan yadda zaka samu data mai sauki cikin kankanin kudi, Wannan data ana amfani dashi cikin dare ne wato Night Browsing wanda kamafani kiran waya na Airtel domin masu kallo a YouTube ko Downloading.Wannan tsari yana da dadin amfani domin masu yawan yin Browsing a internet kullum,  Da wannan tsari zaka iya dauko abubuwa dayawa ko kallon abin dakake so a internet. Idan kana so kayi Night Browsing dole sai kashiga tsarin Airtel Smart Trybe domin dashi ake samun Night Plan,  Idan kana biye damu yau zamu nuna maka yadda zaka koma tsarin Airtel Smart Trybe sannan kasamu damar Airtel Night Browsing.


Yadda Zaka Shiga Tsarin Airtel Smart Trybe

Domin shiga wannan tsari baka bukatar kashe ko naira, Amma idan kafita a tsarin kana so kakoma kafin kwana 30 ( Wata Daya)  zaka kashe N100.


Domin shiga tsarin Airtel Smart Trybe sai kadanna *312# akan wayarka sannan kadanna 1 nantake zaka shiga wannan tsari.


Idan kana son sayen Airtel Night Plan Data sai kadanna *312# sannan kadanna 3 zaka sayi Night Browsing Data nantake. 


Zaka iya sayen 250MB a N25 wato duk MB 250 Airtel zasu dauki N25 da haka zaka iya sayen 1GB A N100 kokuma iya yadda zai isheka. 


Abin Lura: Data na Airtel Night Plan yana awa 5 ne kullum ( 5 Hours ) wato daga 12AM zuwa 5AM idan bakayi amfani dashi ba acikin wadannan awanni Airtel zasu kwashe data daka saya. Don duk abin daza kayi katabbar kayi amfani da Airtel Night Browsing daga 12AM zuwa 5AM dafatan kagane.


Muna fatan wannan post zai yimaka amfani domin yin Night Browsing da layin Airtel.  Mungode.

No comments:

Post a Comment